Mamakon ruwan sama da ya haifar da ambaliya ya hallaka a aƙalla mutane 21 a kasar Maroko.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a yankin Safi da ke gaɓar tekun Atlantika mai nisan kilomita 330 a kudancin Rabat, babban birnin Maroko, a cewar hukumomin ƙasar.
Ruwan saman da aka sheƙa tsawon awa ɗaya ya haddasa ambaliya a gidaje da shaguna, ya toshe hanyoyi a garin Safi da yankunan da ke maƙwbtaka da shi, a yayin da ma’aikatan bayar da agajin gaggawa suke ci gaba da aiki domin ceto mutane.
Maroko na fama da ruwan sama kamar da bakin-ƙwarya da ambaliya a yankin Atlas mai cike da tsaunuka, bayan an kwashe shekara bakwai ana fama da ƙarancin ruwan sama lamarin da ya sa aka kwashe duk ruwan da ke ma’ajiyar ruwa ta yankin
