
Hukumar INEC ta bayyana cewa ƙorafin al’ummar mazaɓar sanatan Kogi ta Tsakiya Natasha Akpoti-Uduaghan na kiranye bai cika ƙa’ida ba.
A makon da ya gabata ne ’yan mazabar Sanatan suka mika ƙorafi ga INEC na buƙatar yi mata kiranye sanatar daga Majalisar Dattawa.
Sai dai, a cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce, koken na kiranye bai cika sharuddan da doka ta tanada ba.
Majalisar Dattawar ta dakatar da Sanata Natasha kan zargin kin bin ka’idojin majalisar bayan zargin neman lalata da ita da ta yi wa Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio.
Dakatarwar ta tayar da kura da kuma bayyana ra’ayoyi daban-daban na ‘yan siyasa da al’ummar ƙasa.