Kotun ɗaukaka ƙara dake Abuja ta tabbatar da hukuncin Kotun Tarayya da ta hana jami’an VIO tsayawa kan hanya domin ƙwace motoci ko kuma ƙaƙaba musu tara.
Kotun ta ce ba ta ga wani dalili da zai sa a rushe hukuncin kotun Tarayya na ranar 16 ga Oktoba, 2024 ba, wanda ya haramta wa jami’an VIO ƙwace motocin direbobi ko yi musu barazana.
A dalilin hakan ne kotun ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar da VIO ta shigar, tana mai cewa ba ta da wasu ingantattun hujjoji.
Idan za’a iya tunawa a baya, mai Shari’a Nkeonye Maha ta kotun tarayya ta bayyana cewa babu wata doka da ta bai wa VIO ikon tsayawa da kwace ko ƙaƙaba tara ga direbobi saboda wani laifi.
Wannan hukunci ya samo asali ne daga karar kare hakkin dan adam da lauya Abubakar Marshal ya shigar.
A cewar mai karar jami’an VIO sun tare shi da karfi a unguwar Jabi ranar 12 ga Disamba, 2023, kuma aka ƙwace motarsa ba tare da wani dalilin doka ba inda ya buƙaci kotu ta tantance ko abin da jami’an VIO ɗin suka yi ba cin zarafi ba ne ko danniya da kuma saɓawa haƙƙinsa na dan Adam.
Kotun, yayin amincewa da bukatunsa, ta umarci VIO da duk jami’ansu su daina ƙwace motoci ko ƙaƙaba tara ga direbobi, domin hakan ba bisa ka’ida ba ne, kuma danniya ce.
