
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta koma aikin ta a matsayin ‘yar majalisar Dattajai bayan karewar wa’adin dakatar da ita da Majalisar ta yi na watannin shida
Majalisar ta dakatar da Sanatan mai wakiltar Kogi ta tsakiya a matsayin ladabtarwa na abin da suka kira karya dokarsu a zauren majalisa. Maris 2025.
Rahotanni sun ce tun a ranar 23 ga watan Agusta aka ga an buɗe ofishinta na majalisa da aka rufe, amma sai a yau 7 ga wata ta shiga tare da kama aiki yadda ya kamata.
A ranar 20 ga watan Fabrairu shekarar 2025 aka fara samun takun saƙa tsakanin Natasha da shugaban majalisar Sanata Akpabio, inda ta ƙi amincewa da canjin kujerar da ya umarceta ta yi, hakan kuma ya haifar da cece-kucen da aka ce ya saba wa dokar majalisa.
Majalisar ta kuma yanke hukuncin dakatar da ita daga zauren da kuma shiga harabar baki dayansa tsawon wata shida. Hakan na nufin dakatar da albashinta da kuma alawus-alawus dinta da masu yi mata hidima.
Hakan ya haifar da ƙararraki a kotu, inda Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta yanke hukunci a watan Yuli 2025 cewa hukuncin hanata aiki ba ya cikin tsarin mulki, inda ta umarce majalisar da ta dawo da ita.
Cece-kuce tsakanin Natasha da shugabancin majalisar ya samo asali daga zargin da ta yi masa na cin zarafinta, majalisar kuma dage kan cewa ba shine dalili ba, face rashin biyayya ga umarnin majalisar.
Natasha na ɗaya daga cikin mata huɗu kacal a majalisar dattai mai mambobi 109. Ta kuma lashi takobin ci gaba da yaki da rashin adalci da cin zarafin mata a majalisar.