Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya taya mabiya addinin Kirista a jihar da Najeriya gaba daya murnar bikin Kirsimetin shekarar 2025, yana mai bayyana lokacin a matsayin na ƙauna, sadaukarwa, haɗin kai da zaman lafiya.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanyawa hannu.
Gwamnan ya ce bikin na Kirsimeti yana bada damar tunani kan muhimman ɗabi’un zaman lafiya, haƙuri, tausayi da hidima ga al’umma.
Gwamna Yusuf ya buƙaci mabiya addinin na Kirista da su yi amfani da lokacin bukukuwan wajen ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kai da cigaba, tare da kira ga dukkan mazauna jihar, ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba, da su ci gaba da zama cikin mutunta juna da fahimta.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na tabbatar da aniyar gwamnatin sa na kare haƙƙin kowane ɗan ƙasa, da samar da yanayi mai kyau yanda kowa zai iya gudanar da addininsa cikin kwanciyar hankali, tare da kira ga shugabannin addinai da su ci gaba da yin wa’azi kan haƙuri da zaman tare a tsakanin al’umma.
