Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewa ya ga motocin kayayyakin agaji da dama da aka adana a Jordan, suna shirin shiga Gaza domin isar da su ga jama’a.
Kakakin asusun, Rosalia Bollen, ta tabbatar wa BBC cewa suna fatan hanyoyin da aka bi wajen isar da kayayyakin za su taimaka wajen tsagaita wuta a yankin.
Sai dai ta bayyana cewa, ko da kayayyakin sun isa Gaza, raba su zai zama babban kalubale saboda yadda sojojin Isra’ila suka wargaza hukumar a birnin da Isra’ila ta yi luguden wuta babu iyaka.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta kuma bayyana cewa halin da ake ciki a Gaza yana ƙara tsananta, inda kusan kashi 91 cikin 100 na mutanen yankin ke fama da matsalar rashin abinci.
Wannan mataki na zuwa ne a lokacin da aka cimma yarjejeniyar kawo karshen harin ta’addanci da Isra’ila ke kaiwa ga kasar Falasdinu.