
Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya kira Muhammadu Sunusi na II da Sarkin Kano.
Kashim Shettima ya faɗi hakan yayin Taron Koli Kan Tattalin Arziki da ake yi a Abuja a inda Sarkin ya ke daya daga cikin manyan bakin a taron na masu fada a ji fannin tattalin arziki.
Rahotanni sun nuna cewa Mataimakin Shugaban Kasa kira sunan Sarkin ne yayin da yake karanto sunayen manyan bakin a jawabinsa a matsayin gaisuwa wanda hakan ya yi nuni da watakila ga sauyin matsayi kan danbawar masarautar Kano.

.