Kashim Shettima ya ƙaddamar da jirgin ruwa samar da man fetur a Dubai.
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya kaddamar da jirgin ruwa mai samar da man fetur Dubai.
Jirgin, mallakin kamfanin Oriental Energy zai iya adana ganga miliyan ɗaya na man fetur, kuma zai fara ne da samar da ganga 17,000 a rana kafin ya ƙara zuwa ganga 30,000.
Ana kuma sa ran jirgin zai iso Najeriya a farkon shekarar 2025.
Da yake jawabi yayin kaddamar da jirgin, Kashim Shettima Shettima ya ce hakan wani babban ci gaba ne aka samu a ɓangaren mai da kuma ƙara karfin tasirin Najeriya a duniya.
Ya kara da cewa abin da ya sa Najeriya ta kere wa wasu ƙasashe shi ne ganin yadda ta fahimci inda duniya ta dosa.
An bayyana cewa darajar jirgin ruwan, mai samar da mai ya kai dala miliyan 315.
