Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Cif Femi Fani-Kayode, ya bayyana cewa matsalar kashe-kashen da ake fama da su a sassa daban-daban na ƙasar nan ba su da alaƙa da wani addini.
Fani-Kayode ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi a matsayin bako mai jawabi a taron cika shekaru 35 da kafuwar Cocin Anglican da ke garin Kafanchan a Jihar Kaduna, a ranar Lahadi.
“Lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su dawo daga rakiyar mutanen da ke amfani da addini wajen raba kan al’umma.
“Masu kashe Kiristoci su ne dai ke kashe Musulmi”. In ji shi.
Kayode ya kuma buƙaci mabiya addinan biyu da su rungumi zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna, tare da gujewa duk wani yunƙurin na kawo rarrabuwa ko tashin hankali.
A nasa ɓangaren, Babban Mai Shari’a na Jihar Kaduna, Barista James Kanyip, wanda ya wakilci Gwamnan Jihar, Sanata Uba Sani, ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar na ci gaba da kare ‘yancin addini da tabbatar da haɗin kai da shugabannin addinai, musamman masu wa’azin zaman lafiya da jituwa.
Haka kuma, Sanatan Kaduna ta Kudu, Barista Sunday Marshall Katung, wanda ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Jema’a da Sanga, Hon. Daniel Amos ya wakilta, ya yaba wa Gwamna Uba Sani bisa yadda yake tafiyar da mulki cikin adalci da rashin nuna wariya ga kowane ɓangare na jihar.
