Wani katon Karfe ya fado kasar Kenya daga sararin samaniya
Zagayayyen ƙarfe mai kusan kafa 8 (mita 2.4) mai nauyin kilo 1,100 (kimanin kilogiram 453) ya fado kauyen Mukuku da ke gabashin gundumar Makueni a ranar Litinin.
Hukumar Kula Da Yanayin Sararin Samaniya ta kasar ta ce, lokacin da jami’anta suka je inda karfen ya fado sun same shi da zafinsa.
“Lokacin da muka je wurin mun samu karfen da sauran zafi a jikinsa,” inji Julius Rotich, wani jami’in ‘yan sandan yankin.
Rotich ya shaida wa kafar yada labarai ta kasar Kenya, cewa ‘yan sanda sun killace wurin har sai abin ya yi sanyi.
“Sakamakon binciken farko ya nuna cewa karfen ya balle ne daga jikin wari roka da aka harba,” in ji hukumar.
Sannan ta kuma ce a yanzu “ba shi da wata barazana ga tsaro, tana kuma kokarin tantance ainihin asalinsa karfen.
Akwai dai dubban taurarin Dan Adam da ke shawagi a sararin samaniya don ayyuakn sadarwa da kuma tsaro.
Kawo yanzu babu wata Kasa da ta ba da sanarwar wani ya faru ga taurarin dam Adam dinta ko rokar da ta harba sararin samaniya