Gwamnatin Mali ta sanar da rufe ɗaukacin makarantun ƙasar ciki har da jami’o’i, sakamakon matsalar ƙarancin man fetur da ya addabi ƙasar
Ministan Ilimi na ƙasar Amadou Sy Savane, ne ya sanar da hakan yayin wani jawabinsa ta gidan Talabijin na ƙasar a tun daga ranar Lahadin.
“Za a rufe makarantu har tsawon mako biyu ne a faɗin ƙasar sakamakon matsalar ƙarancin mai, wadda kai tsaye tana shafar zirga-zirgar Malamai, da ma’aikata da kuma ɗalibai wajen zuwa makarantun,” in ji shi.
Rahotanni sun ce ƙarancin man na da alaƙa da ƙaruwar hare-haren ƙungiyar Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin, mai samun goyon bayan al-Qaeda, a yunƙurinta na ƙoƙarin hana shigar da mai cikin ƙasar.
Sai dai duk da wannan ƙarancin mai da ake fama da shi, farashinsa ya ci gaba da kasancewa kamar da, inda ake siyar da lita ɗaya akan CFA 775 kimanin Naira 2,008. 50 yayin da man dizal kuma ake siyar da shi akan CFA 725, kimanin Naira 1878.86.
Yanzu haka dai, ɗalibai a dukkan matakai kama daga Firamare har zuwa Jami’a za su ci gaba da zama a gida har zuwa ranar 10 ga watan Nuwamba mai kamawa, yayin da gwamnatin ƙasar ke kokarin ganin ta shawo kan lamarin.
