
Gwamnatin jihar Kaduna tace karancin jami’an tsaron da ake dasu a kasar nan na daya daga cikin abunda yake kawo matsalar rashin tsaron.
Gwamnan jihar Malam Uba Sani shi ne ya bayyan hakan a lokacin da yake jawabi a wajan taron kaddamar da littafin Sheik Abubakar Muhmud Gumi wanda ya guduna a jihar Kaduna.
Yace akwai bukatar malaman kasar nan su ci gaba da hada kan su waje gudu domin tallafa yinkurin gwamnatin da kuma hukumomin tsaro domin magance matsalar.
Gwamna Malam Uba Sani ya kara da cewa, matsalar rashin tsaron da yake faruwa a Arewacin kasar nan nada alaka ne da yadda al’umma suka yi watsi da junan su.
Daga bisani gwamnan ya riko masu ruwa da tsaki dasu cire siyasa daga cikin alamuran tsaro domin samun zaman lafiya a kasar nan.