Gwamnan Borno ya roƙi gwamnatin Tarayyar da cewa kar ta bari Boko Haram ta ƙwace garin Marte
Gwamnan jihar Babagana Umara Zulum, ya roƙi Gwamnatin Tarayyar ne da ta samar da ƙwararan dabarun da za su tabbatar da cewa garin Marte bai faɗa hannun mayaƙan Boko Haram da ISWAP ba.
Zulum, wanda da shi aka yi ta tsare-tsaren ayyukan tsaro har cikin tsakar dare a ranar Asabar, ya gudanar da rangadi don tantance ƙalubalen da aka fuskanta a Marte, tare da lalubo hanyoyin da za a bi don samar da zaman lafiya.
Kafin zuwan Zulum, duk jama’ar cikin garin Marte sun tsere gaba ɗaya bayan harin da mayaƙan Boko Haram suka kai ranar Juma’ar da ta gabata, inda dubbai suka fake a garin Dikwa.
Da yake magana da manema labarai a ranar Lahadi, gwamnan ya jaddada cewa ziyarar da ya kai Marte ta kasance domin samar da haɗin-kan al’umma da juriya da kuma ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro ne.
“A shekara huɗu da suka wuce ne aka sake mayar da al’ummar Marte garinsu, amma abin takaici, a cikin kwanaki ukun da suka gabata, an sake tarwatsa su tare da sake sa mutanen garin yin gudun hijira.
“Mutane kusan 20,000 ne suka bar Marte zuwa Dikwa,wannan adadi mai yawa barazana ce domin barinsu su zauna a sansanin na iya sanya mafi akasarin matasa su shiga cikin mawuyacin hali da kuma yiwuwar masu tayar da ƙayar bayan sun sanya su a cikinsu.
“Kawo yanzu Karamar Hukumar Marte ta ƙunshi garuruwa da ƙauyuka sama da 300, a yanzu muna da matsayi ɗaya kawai, idan ba za mu iya kula da wannan ba, to za mu rasa dukkanin ƙananan hukumomin ga ‘yan tayar da ƙayar baya, wanda hakan zai yi matukar tayar da hankali, kuma ina ganin ba za mu bari hakan ya faru ba, don haka ina kira ga Gwamnatin Tarayya da Rundunar Sojojin kasar nan, mu hada kanmu domin wannan gari ya ci gaba da zama a hannunmu.”
Gwamnan ya jaddada ƙudirinsa na tallafa wa jami’an tsaro wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar Borno,
