Gwamnatin jihar Kano tana sa ran yiwa yara fiye da miliyan 4 allurar rigakafin cutar shan inna a kananan hukumomi 44 na jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai.
“Wannan yunkurin wani muhimmin mataki ne da gwamnati ke dauka domin tabbatar da cewa cutar Polio ta ci gaba da zama tarihi a jihar nan.
“Ma’aikatar lafiyar ta samar da isasshen kayan aiki da alluran rigakafi, tare da tura ma’aikata zuwa dukkan kananan hukumomi 44.
Kwamishinan ya bukaci iyaye da masu kula da yara da su bai wa ma’aikatan lafiya hadin kai, domin ganin wannan shirin ya samu nasara kamar yadda aka tsara shi.
Sannan ya kuma yaba wa kungiyoyin hadin gwiwa da hukumomin lafiya na cikin gida da na kasa-da-kasa bisa gudunmuwar da suke bayarwa wajen yakar cutar a jihar.
