 
        Jihar Kano ta shiga jerin jihohi Bakwai a kasar nan da za su iya rike kansu ko ba tallafi daga gwamnatin tarayya, kamar yadda rahoton cibiyar ta budget IT ya bayyana.
Rahoton ya ce, adadin kuɗin da jihohi ke samu a kasarnan daga kason tarayya ya kusan ninkawa idan aka kwatanta da kafin 2023, sakamakon cire tallafin man fetur.
Yawancin jihohin na dogara ne da kuɗaɗen da suke samu daga gwamnatin tarayya, wanda ake rabawa a kowane wata, tsakanin gwamnatin tarayya da jihohin da kuma ƙananan hukumomi.
To sai dai akwai jihohin da ke ƙoƙorin samar wa kansu hanyoyin dogaro da kai ta hanyar inganta karɓar haraji da inganta kasuwanci domin dogaro da kansu.
Jihar Legas ce kan gaba cikin jihohin da suka fi samun kuɗin shiga, kamar yadda shafin BudgtIT ya nuna.
A shekarar 2024 da ta gabata jihar ta samu kuɗin shiga da ya kai Naira tiriliyan 1.26, ƙarin kashi 50 cikin 100 na abin da ta samu a shekarar 2023, kamar yadda BudgetIT ya nuna.
Sai Jihar Enugu da ke yankin kudu maso gabashin kasar nan da Arzikin da jihar ta samu a cikin gida a 2024 ya kai naira biliyan 180.50, ciki har da naira biliya 26.68 da ta samu ta hanyar biyan haraji.
Bisa alƙaluman da hukumar ƙididdiga ta Najeriya, NBS ta fitar sun nuna jihar Kano ta samu kuɗin shiga na cikin gida har naira biliyan 74.77 a shekarar 2024, saɓanin naira biliyan 37.38 a 2023 wanda yasa ta zama ta uku a jerin.
Jihar Kaduna ita ce ta hudu da ta samar da naira biliyan 71 na harajin cikin gida a shekarar da ta gabata ta 2024.
Sauran jihohin sun hada da Kwara Anambra da Abia.
Masana tattalin arziƙi sun sha faɗin cewa jihohi da dama za su rayu ko da kuwa babu tallafin gwamnatin tarayya, idan har za su cire son zuciya sakamakon rashawa da cin hanci da suka baibaye harkokin gwamnati.

 
           
           
           
           
         
         
         
         
         
         
           
          