
Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Tuntuba Ta Arewa Consultative Forum (ACF) kan yunƙurinta na kafa sabuwar majalisar dattawan Kano, tana mai jaddada cewa tuni tana da irin wannan majalisa a ƙarƙashin gwamnatin jihar.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Malam Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.
Wayya ya bayyana cewa tun a watan Janairun 2024 ne Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa majalisar dattawan Kano domin bayar da shawara kan ci gaban al’umma.
Sanarwar ta kuma ce, ana ci gaba da shirye-shiryen tabbatar da ingantaccen tsarin da zai bai wa majalisar damar fara aiki yadda ya kamata.
An kuma bayyana cewa ba ta da alaƙa da siyasa ko jam’iyya, sai dai dandalin bayar da shawarwari bisa hikima da gogewa.
Majalisar za ta ƙunshi fitattun ‘yan Kano, ciki har da tsofaffin shugabanni, alƙalai, malamai, sarakuna, ‘yan kasuwa da shugabannin tsaro.
Gwamnatin ta bukaci ƙungiyoyi da sauran jama’a da su haɗa kai da tsarin da aka kafa maimakon ƙirƙirar sabon tsari, domin ƙarfafa ayyukan majalisar da kuma cimma burinta na kawo ci gaba da haɗin kai a jihar.
Sanarwar ta ƙara da cewa nan ba da jimawa ba za a kammala duk shirye-shiryen kafa majalisar kafin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da ita.