Hukumar Kula Da Alhazai Ta Kasa, NAHCON ta sanar da zaben kamfanonin jiragen sama guda hudu don aikin jigilar mahajjatan Hajjin wannan shekara.
Kamfanonin su ne Air Peace Limited da Fly-Nas da Max Air da kuma UMZA Aviation Services Limited.
Kamfanonin sun samu nasara ne bayan tantancesu daga cikin masu neman izini 11 da kwamitin tantancewa na hukumar ya yi.
Kwamitin tantancewa mai mambobi 32, ya hada da kwararrun masana jiragen sama da wakilan hukumomin NCAA da FAAN, da kuma ICPC,
Ya kuma gudanar da aikin tantancewar ne tun cikin watan Nuwamba 2024.
Haka nan kuma, kwamitin ya zabi kamfanonin jigilar kaya guda uku don ayyukan na hajjin bana.
Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya taya kamfanonin da suka yi nasara murna tare da jan hankalinsu kan cika alkawuran da suka dauka