Shugabannin Hamas sun ce tsoma bakin Donald Trump a rikicin Gaza na kara dagula batun yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.
A jiya Litinin, Trump ya yi barazanar watsi da yarjejeniyar, matuƙar Hamas ta kasa sakin dukkan ‘yan Isra’ila da take garkuwa da su.
Mai magana da yawun Hamas, Sami Abu Zuhri, ya ce hanya ɗaya tilo ta ganin an saki fursunoni ita ce martaba yarjejeniyar da aka cimma a watan jiya.
Hamas ta yi barazanar jinkirta sakin sauran fursunonin da take riƙe da su, tana zargin Isra’ila da take ƙa’idojin yarjejeniyar.
Ƙungiyar ta ce Isra’ila na hana shigar kayan agaji zuwa Gaza, tare da kin sakin wasu Falasɗinawa da ke tsare a hannunta.
Isra’ila ta musanta zargin, sannan ta ƙara jibge dakarunta a kusa da yankin.
