Sabon rahoton ƙungiyar Tarayyar Turai ya bayyana cewa fiye da jami’an ‘yan sandan Najeriya 100,000 na aiki wajen kare manyan ‘yan siyasa da fitattun mutane a maimakon al’umma daga miyagun laifuka.
Rahoton, wanda Hukumar Tarayyar Turai kan lamuran mafaka ta wallafa a watan Nuwamba, ya kiyasta cewa Najeriya na da jami’an ‘yan sanda 371,800 domin hidimar al’umma fiye da miliyan 236.
Sai dai an karkatar da kaso mai tsoka daga cikinsu zuwa gadin manya, wanda ke haifar da ƙarancin jami’an sintiri da tsaron al’umma.
Sakamakon wannan, rahoton ya nuna cewa, akwai jinkirin amsa kiran gaggawa idan laifi ya faru, yankuna da dama ba su da jami’an tsaro, laifuka na ƙaruwa ba tare da ɗaukar mataki da wuri ba.
EU ta kuma nuna damuwa kan cin hanci, amfani da ƙarfi fiye da kima, kama mutane ba bisa ƙa’ida ba, da ƙarancin kayan aiki a rundunar ‘yan sanda.
Masana na ganin cewa muddin ba a sauya tsarin amfani da jami’an tsaro daga kare masu mulki zuwa kare talakawa ba, matsalar tsaro a Najeriya za ta ci gaba da dagulewa, musamman a yankunan karkara.
