Ƙungiyar Dillan mai ta Dappman ta bayyana damuwa kan rikicin da ya taso tsakanin Matatar Man Fetur ta Dangote da Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas (NUPENG).
ƙungiyar ta jaddada muhimmancin sasanta rikicin domin kauce wa shafar al’ummar Najeriya, musamman a lokacin da ɓangaren rarraba man fetur ke fara samun daidaito bayan cire tallafi.
A wata sanarwa da sakataren zartarwa na DAPPMAN, Olufemi Adewole, ya fitar a ranar Asabar, kungiyar tace ko da yake ’yan kasuwa suna maraba da zuwan Matatar Dangote, gudunmawar ta ga bukatun kasar nan bai wuce kashi 30 zuwa 35 cikin 100 ba.
Ya kara da cewa sauran kason, har yanzu DAPPMAN da sauran masu shigo da mai ne ke kawowa da rarrabawa
NUPENG ta yi barazanar shiga yajin aiki saboda shirin Matatar Dangote na fara rarraba man kai tsaye, wanda ƙungiyar ke adawa da shi, tana mai cewa matatar na ƙoƙarin hana direbobin motocin ɗaukar man ta shiga kowace ƙungiya.
Sai dai Hukumar DSS ta shiga tsakani domin shawo kan lamarin.
