
Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (DSS) ta gurfanar da wasu manyan kwamandojin ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, bisa zargin aikata munanan laifuka masu nasaba da ta’addanci, sace-sace, da fashi da makami.
Wadanda aka gurfanar su ne Mahmud Usman, wanda aka fi sani da Abu Bara’a Abbas ko Mukhtar, da mataimakinsa Mahmud Al-Nigeri, wanda aka fi sani da Malam Mamuda.
DSS ta bayyana cewa dukkansu su ne manyan kwamandojin ƙungiyar Ansaru wani rukunin da ya samo asali daga Boko Haram, kuma ana danganta shi da al-Qa’ida.
A zaman kotun da aka gudanar yau Alhamis, mai shari’a Emeka Nwite ya karɓi takardar tuhuma da ke ɗauke da shafuka 32 na hujjoji da DSS ta gabatar, waɗanda suka ƙunshi cikakken bayani game da laifukan da ake zargin waɗannan kwamandoji da su.
Cikin tuhume-tuhumen da waɗannan kwamadoji na Ansaru ke fuskanta har da kitsa ɓalle gidan yarin Kuje a cikin watan Yulin 2022 wanda ya kai ga tserewar fursunoni fiye da 600, Sace Injiniyan Faransa, Francis Collomp, a 2013 da kuma Alhaji Musa Umar Uba, Magajin Garin Daura, a 2019.
DSS ta bayyana cewa Mahmud Al-Nigeri ya samu horo tsakanin 2013 zuwa 2015 a wasu sansanonin horo na masu tayar da ƙayar baya a ƙetare