Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar ya ce, Najeriya ta soma tattaunawa da Amurka bayan barazanar Trump na kawo wa Najeriya hari a bisa zargin kisan kiristoci a kasar.
A wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, Minista Tuggar ya ce, tattaunawar na mayar da hankali ne kan yadda Najeriya da Amurka za su haɗa kai wajen magance matsalolin tsaro domin amfanin duniya baki ɗaya.
A farkon watan Nuwamba, Trump ya bayyana cewa ya bai wa ma’aikatar tsaron Amurka umurnin ta soma tsara yadda za a kai hari Najeriya.
Sai dai Ministan ya ce, ba ya ganin Amurka za ta aiwatar da hakan, yana mai cewa tattaunawar na ci gaba kuma an samu wasu ci gaba a cikin sa.
Trump ya yi gargadin cewa addinin Kirista na fuskantar barazana a Najeriya, yana mai cewa idan har ƙasar ba ta kawo ƙarshen kashe-kashen ba, Amurka na iya kai hari a nan gaba.
