Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya bayyana damuwarsa kan barazanar da shugaban Amurka Donald Trump na kawo wa Najeriya hari kan zargin kisan kiristoci.
Obi ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa a dandalin sada zumunta na X yammacin Litinin.
“Wannan barazana abu ne mai tayar da hankali ga dukkan ’yan Najeriya masu kishin ƙasa.
Amurka za ta iya turo sojojinta su yaƙi ta’addanci a Najeriya, tare da sanya ƙasar cikin jerin ƙasashen da Amurka ke nuna damuwa da su, ya kamata su zama gargaɗi ga gwamnati da kuma ‘yan Najeriya gaba ɗaya”. In ji shi.
Obi ya kuma bayyana cewa matsalar tsaro da ake fama da ita a ƙasar za a iya shawo kanta ne ta hanyar shugabanci na gari, yana mai cewa duk da cewa matsalar ba ta fara ne a wannan gwamnatin ba, amma akwai rashin ƙwarewa da rashin taka-tsantsan wajen magance ta.
Sannan ya ce, Najeriya da Amurka na da dogon tarihin alaƙa mai kyau, bai kamata a watsar da wannan alaƙar ba a yanzu.
