
Gwamnatin Tarayyar ta yi gargadin cewa za a fuskanci ambaliyar ruwa mai tsanani a jihohi 30 da babban birnin tarayya Abuja a daminar 2025.
Ministan Albarkatun Ruwa, Joseph Utsev ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin gabatar da hasashen ambaliyar ruwa da hukumar NIHSA ta yi.
“Jihohin da za su fuskanci wannan mummunan hadari sun hada da Legas da Ogun da Abia da Ondo da Adamawa da Akwa Ibom da Anambra da Bauchi da Benue da Borno da Bayelsa da Cross-River da Delta da Ebonyi da Edo da Gombe da Imo da Jigawa da Kebbi da Kogi da Kwara da Nasarawa da Neja da Osun da Oyo da Rivers da Sokoto da Taraba da Yobe da Zamfara da kuma Abuja.
“Wasu yankuna na kudu maso kudancin kasar nan, musamman Bayelsa da Cross-River da Delta da Akwai-Ibom da Edo da kuma Rivers, suna cikin hadarin ambaliya ta gabar tafkuna da rafuka.” In ji ministan.
Joseph Utsev ya bayyana cewa ambaliyar ruwa na daga cikin manyan masiffofin yanayi da ke shafar rayuwar mutane da albarkatun kasa a Najeriya.
Ya kuma jaddada cewa, sauyin yanayi yana kara tsananta hadarin ambaliyar ruwa a wasu jihohi.
Sannan Ministan ya ce, jama’a su dauki matakan kariya da kuma sanya idanu a kan rahotannin yanayi domin rage illolin ambaliyar ruwa.