Lamarin ya fari ne a Sai Paulo daya daga cikin manyan biranen ƙasar a karshen mako.
Jirgin karami ne wanda ya yi kokarin saukar gaggawa a titin Marques de Sao Vincent mai cinkuso na birnin ya kuma yi taho-mu-gama da motar haya Bas mai dauke da fasinjoji.
Shafin BBC na Turanci ya rawaito cewa, an garzaya da daya daga cikin fasinjojin motar zuwa asibiti.
Shi kuma wani Mai Babur ya samu rauni sakamakon buguwa da wani Karfe da ya balle daga jikin jirgin ya same shi.
Amma dukkanin wadanda suke cikin jirgin wadanda ba a fadi yawansu ba sun hallaka
A cewar Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa Kyaftin Crispin Major.
