Rundunar sojin saman Koriya ta Kudu ta ce ta dakatar da mafi yawan jiragen samanta, bayan da wasu jiragen yaƙi suka yi kuskuren jefa makamai kan wasu tankokin mai a lokacin wani atisaye a farkon makon nan.
An jefa makaman ne a wani wuri da fararen hula ke harkokinsu, mai nisa kilomita 100 daga gabashin Seoul, babban birnin ƙasar.
Ba a dai samu labari rasa rai ko jikkata a lokacin harin ba. Amma ƙasar ta dakatar da babban atisayen haɗin gwiwa da take yi da Amurka. Atisayen da aka yi wa laƙabi da ”Tutar Ƴanci” ana yinsa ne sau biyu a shekara, tare da jiragen sama fiye da 90.
A watan Maris wasu jiragen ƙasar biyu sun yi kuskuren jefa boma-bomai a wani yankin fararen hula, yayin wani atisayen lamarin da ya yi sanadiyyar jikkata fiye da mutum 50.
