Gwmantin jihar Benue ta tabbatar da mutuwar mutane 45 a ƙauyen Yelewata dake jihar, sakamakon harin da ƴan bindiga suka kai da safiyar ranar Asabar.
Kakakin ofishin gwamnan jihar Tersoo Kula ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa jami’an gwamnatin jihar da Kwamishinan ƴan sanda sun ziyarci Ƙauyen inda suka tabbatar da mutuwar mutane 45 a harin da ya danganta da kabilanci.
Sai dai mazauna yankin da dama sun shaidawa AFP cewa suna fargabar mutanen da suka mutu za su haura 100.
Wani mazaunin garin Amineh Liapha Hir ya shaida wa AFP cewa lamarin akwai tada hankali, la’akari da cewa mutane da yawa sun mutu, tare da kona gidaje da dama.
Shi ma wani mazaunin yankin, Christian Msuega, wanda ya ce ya tsallake rijiya da baya, amma ƴaƴansa da sirikinsa sun mutu, bayan da aka kone da ransa. Shi ma ya ce yana tunanin mutane kusan 100 ne suka mutu, ya kuma zargi Fulani makiyaya da kai harin.
Kakakin ƴan sandan Udeme Edet ya tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP harin, kuma ya ce ƴan sandan sun yi artabu da maharan.
