Gwamnan jihar Neja ya ce gwamnatinsa za ta sayi makamai domin bai wa dakarun rundunar tsaron dazukan jihar 10,000 da za ta kafa.
Gwamna Mohammed Umaru Bago ya bayyana haka a hirar sa BBC, yana mai cewa tuni suka fara bai wa matasan rundunar horo.
Ya ce burinsu shi ne su ɗauki matasa 1,000 daga kowace ƙaramar hukuma domin kare kansu.
- Sojoji sun kashe ‘yan ta’dda da kwace muggan makamai a jihar Neja
- ’Yansanda sun kama mutane 9 da laifin garkuwa da kansu a Neja
Ya ce za su sayi makamai sosai, domin baiwa dakarun damar tunkarar ‘yan ta’addan.
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta yi hakan ne tare da haɗin gwiwar gwamnatin tarayya domin ƙirƙirar rundunar mai suna Forest Guard, wadda za ta dinga saka ido da kuma tsare dazukan jihar masu faɗin gaske.
Gwamna Bago ya ce ‘yanbindigar na kwarara ne daga jihohin Zamfara da Kaduna maƙwabtan jihar.
Jihar Neja na cikin wuraren da suka fi fama da hare-haren ‘yanbindiga da ke kashewa da kuma kama mutane domin neman kuɗin fansa, baya ga mayaƙan ƙungiyar Boko Haram da suka ɓulla sassan jihar.
