
Tsohon ɗan Majalisar Tarayya, Sanata Abubakar Sadiq Yar’adua, ya fice daga jam’iyyar APC a hukumance zuwa jamiyyar ADC.Yana mai danganta matakin da gazawar shugabancin jam’iyyar da kuma rashin iya mulki da gwamnatin tarayya ke yi.
A wata wasikar da ya aike wa Shugaban mazabar sa ta jam’iyyar APC, mai ɗauke da kwanan wata 28 ga watan Yulin wannan shekara,
Sanata Yar’adua ya bayyana takaicin sa matuƙa kan yadda jam’iyyar ke tafiya da kuma rawar da take takawa a cikin rikicin tattalin arziki da zamantakewa da ke kara tabarbarewa a ƙasar.
Yar’adua ya caccaki gwamnatin jam’iyyar APC da cewa “gaskiya ta lalace, tana da son kai kuma cike take da cin hanci,” yana mai cewa jam’iyyar yanzu ta zama abin kunya ga ƙa’idojin da aka gina ta a kai.
Ya kuma tuna da irin sadaukarwar da ya yi tun daga kafuwar Congress for Progressive Change (CPC), har zuwa lokacin da aka kafa APC, wadda ta yi nasarar kifar da gwamnati PDP.
Sanatan ya zargi shugabancin jam’iyyar da nuna halin ko-in-kula a kan matsalolin tsaro, wahalar tattalin arziki da kuma cin zarafin jama’a da ke ƙaruwa a kullum, yana mai cewa ‘yan Najeriya na ci gaba da wahala yayin da shugabannin ke fifita muradun masu rike da madafun iko.