Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jigawa ta mikawa NAHCON Naira biliyan 4.5 kudin aikin hajjin wannan shekarar.
Babban Daraktan hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya bayyana haka a Dutse.
Ya ce, ana sa ran biyan karin kudi kafin cikar wa’adin da NAHCON ta bayar.
Jihar ta samu kujeru 1,809, inda aka raba kashi 40 cikin 100 ga kananan hukumomi.
Labbo ya bukaci maniyyata da su gaggauta biyan kudinsu domin kada su rasa kujerun.
