Wani matashi mai shekaru 27, Kabiru Nuhu, da ake zargi da kashe mahaifinsa ta hanyar kone shi da wuta a karamar hukumar Kazaure ta jihar Jigawa, ya bayyana abin da ya sa ya aikata hakan.
Rahotanni sun ce an kama wanda ake zargin ne bayan ya zuba fetur a jikin mahaifinsa tare da banka masa wuta.
A yayin da ‘yan sanda ke bincike, wanda ake zargin ya ce matsalolin cikin gida da kuma sakacin da ya dade yana fuskanta daga mahaifinsa ne suka sa ya dauki wannan mataki.
“Tun da dadewa muke samun sabani da mahaifina, hakan ya sa ya yi watsi da ni ya kuma sakar min rayuwa,” in ji shi.
Ya kara da cewa: “Ban ji dadin halin da nake ciki ba, shi ya sa na yanke shawarar aikata hakan.”
Rahotanni sun nuna cewa an kama shi da raunukan konewa a jikinsa, sanye da jan wando, wanda ya dace da bayanin da marigayin ya bayar kafin rasuwarsa.
Wasu ‘yan uwa sun ce mahaifin da dan nasa sun dade ba sa ga miciji, sama da shekaru biyu, inda suka kara da cewa matashin na fama da rashin kulawa daga iyali.
Sai dai bincike ya kuma gano cewa ana zargin matashin da shan miyagun kwayoyi, lamarin da ake cewa shi ne ya sa mahaifin ya kaurace masa bayan kokarin jan hankalinsa don ya gyara halayensa ya ci tura.
Hukumomi sun ce bincike na ci gaba da gudana kan lamarin.
