Dan Majalisar Dokokin Amurka, Riley M. Moore, ya bukaci a kakaba takunkumi tare da soke dokokin da suka tanadi hukuncin kisa ga wanda yayi batanci ga Annabi Muhammad (SAW) a Najeriya, a matsayin wani bangare na shawarwarin da ya ce za su taimaka wajen dakile hare-hare kan Kiristoci a kasar.
Moore ya bayyana hakan ne cikin wani rahoto da ya gabatar wa Fadar White House, sannan ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata.
Rahoton, wanda ya ce ya biyo bayan watanni na bincike, ya kunshi matakai da ya bayyana a matsayin hanyoyi na kawo karshen abin da ya kira tsanantawa da ake yi wa Kiristoci a Najeriya da kuma dakile tashe-tashen hankulan masu tsattsauran ra’ayi.
A cewarsa, binciken ya hada da ziyarar hadin gwiwa ta ‘yan majalisa zuwa Najeriya, zaman sauraron bayanai daga kwararru, tattaunawa da shugabannin addini, ganawa da ‘yan gudun hijira (IDPs), da kuma tattaunawa da manyan jami’an gwamnatin Najeriya.
- Muna da kyakkyawar fahimtar juna da kasar Amurka-Gwamnatin Tarayya
- ‘Yan Majalisar Amurka Sun Gana Da Ribadu A Abuja
Moore ya ce: “Bayan ganawar da muka yi a White House, ina godiya ga Shugaba Trump saboda sake ayyana Najeriya a matsayin Kasar da ke da Matukar Damuwa (Country of Particular Concern), da kuma kudurin gwamnatinsa na kare ‘yan’uwanmu Kiristoci daga tsanantawa.”
Ya kara da cewa ya ziyarci Najeriya tare da tawagar hadin gwiwa ta ‘yan majalisa inda ya ce ya shaida da idonsa irin kalubalen tsaro da hare-haren da Kiristoci ke fuskanta.
An sake ayyana Najeriya a matsayin Kasar da ke da Matukar Damuwa (CPC) a ranar 31 ga Oktoba, 2025. Moore ya ce wannan mataki ne ya sa aka ba shi da Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai, Tom Cole, alhakin jagorantar cikakken bincike kan halin da ake ciki.
Rahoton ya ba da shawarar kulla yarjejeniyar tsaro ta musamman tsakanin Amurka da Najeriya domin kare al’ummomin Kiristoci da ake ganin suna cikin hadari, tare da rushe hanyoyin sadarwa da ayyukan kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi.
Haka kuma ya ba da shawarar a dakatar da wasu tallafin kudaden Amurka a wasu bangarori har sai gwamnatin Najeriya ta dauki kwararan matakai na dakile hare-hare kan Kiristoci.
Moore ya kuma bukaci a kakaba takunkumi da hana biza ga mutanen da ake zargi da hannu ko goyon baya wajen tsanantawa addini.
Bugu da kari, ya bukaci hadin gwiwa da kasashe irin su Faransa, Hungary da Birtaniya domin tinkarar matsalolin tsaro a Najeriya.
Moore ya ce ta hanyar zaman sauraro da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, sun samu cikakken bayani kan barazanar tsaro da halin da Kiristoci ke ciki a Najeriya.
A ranar 7 ga Disamba, tawagar ‘yan majalisar ta gana da Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, a Abuja domin tattauna hanyoyin kawo karshen kashe-kashen fararen hula da kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi ke yi.
