
Ana shirin gudanar da jana’izar marigayi Aminu Danatata a birnin Madina ta ƙasar Saudiyya a yau Talata da La’asar.
Tuni tawagar gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, da ta gwamatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf da kuma sarkin Kano Muhammadu Sunusi suka isa Madina domin halartar jana’izar.
Wata tawagar ta Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin da kuma tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da tashi zuwa birnin na Madina da maraicen Litinin.
Rahotanni sun nuna cewa, Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero tuni ya isa Madina tun ranar Juma’a da dare don halartar sutura da kuma jana’izar attajirin dan asalin Kano.
A tawagar gwamnatin tarraya da akwai Ministan Shari’a Prince Lateef Fagbemi da Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris da Ƙaramin Ministan Samar da Gidaje Yusuf Abdullahi Ata.
Fitattun malaman addinin Musulunci a tawagar sun haɗa da Dr. Bashir Aliyu Umar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Khalifa Abdullahi Muhammad.
Ana sa ran Jana’izar a Madina tana cike da daraja da girmamawa ga rayuwar marigayin wanda ya kasance ginshiƙi a harkar kasuwanci da ci gaban al’umma.
Ana sa rai za a binne attajirin kusa da matarsa Rabi’a Dantata, kamar yadda ya buƙata a wasiyyarsa.
