Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce rikice-rikicen cikin gida da ke addabar yawancin jam’iyyun adawa na nuna ƙarara cewa ba su shirya jagorancin ƙasa ba.
Ya bayyana haka ne a Abuja yayin da yake jawabi kan muhimman batutuwan da suka shafi tafiyar da al’amuran zamantakewa, siyasa da tattalin arzikin ƙasa.
Ya ce duk wata jam’iyya da ta kasa tafiyar da harkokinta na cikin gida, ta kasa sasanta sabanin ra’ayoyi, tabbatar da da’a ko kuma gina haɗin kai tsakanin mambobinta, ba za a iya amincewa da ita ta jagoranci ƙasa mai sarkakiya kamar Najeriya ba.
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Abimbola Tooki, ya sanya wa hannu, shugaban ya ce rikice-rikicen da suka haɗa da rarrabuwar kawuna, faɗace-faɗacen cikin gida, shari’o’i da kuma “rashin ingantacciyar akida” da ke addabar jam’iyyun adawa a yanzu, ba wai matsalolin siyasa kawai ba ne, illa alamu ne na raunin tsari da gazawar shugabanci.
Ya ƙara da cewa zai zama haɗari kuma rashin sanin abinda ya dace a siyasa idan aka ba irin waɗannan yan siyasa damar jagorantar Najeriya, alhali sun gaza kiyaye tsari a cikin jam’iyyunsu.
Ya ce: “Jam’iyyar da ba za ta iya tafiyar da kanta ba, ba za ta iya jagorantar Najeriya ba. Idan jam’iyya na fama da rikice-rikicen da ta jawo wa kanta, tana durƙushewa sakamakon rashin kyakkyawan tsari, to bai kamata ta nemi amanar jagorancin ƙasa ba.”
Shugaban APC ya kuma buƙaci yan Najeriya da su rika yin taka-tsantsan, su bambance tsakanin hayaniya da ƙwarewa, farfaganda da shiri da kuma son kai da sahihin shugabanci.
