Jam’iyyar ADC ta ce kawancenta da PDP a matakin kasa wani mataki ne da zai saukaka mata kawo karshen mulkin Bola Tinubu a zaben 2027.
Da yammacin ranar Laraba ne shugabannin ADC da na PDP ɓangaren Kabiru Tanimu Turaki suka yi wata tattaunawar sirri a Abuja.
Cikin waɗanda suke halartar taron akwai Sanata David Mark shugaban ADC na ƙasa da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso, da tsohon ɗan takarar shugaban kasa Peter Obi.
Akwai kuma tsohon Ministan shari’ar Abubakar Malami da tsohon sakataren gwamnati Babachir Lawal, da tsohon gwamnan Rivers Rotimi Amaechi da Sanata Aminu Tambuwal.
A ɓangaren PDP akwai Gwamnan Oyo Seyi Makinde da Shugaban tsagin jam’iyyar PDP na ƙasa Farfesa Jerry Gana da tsohon shugaban jamalisar dattawa Adolphus Wabara, Tsohon gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu da wasu sauran Mambobi.
Yayin da ya ke karin haske a kan ganawar da jagororin jam’iyyaun suka yi, shugaban jam’iyyar ADC na jihar Kano Shu’aibu Musa Ungoggo, ya jaddada cewa sakamakon rashin tsaron da kasar nan ke ciki yasa jam’iyyun suke son yakar APC.
