
Ahmad Hamisu Gwale
Jami’iyyar PDP ta sanar da sauya inda za ta gudanar da babban taronta na kasa daga jihar Kano zuwa jihar Oyo.
Wannan na zuwa ne bayan taron kwamitin zartawa na kasa karo na 101 da aka gudanar a birnin tarayya Abuja.
Jami’iyyar ta ce daukar matakin ya zama dole, domin tabbatar da adalci da kuma bawa kowanne bangare dama domin a dama da shi.
Da fari an tsara taron zai gudana a jihar Kano, sai dai yanzu an mayar da shi zuwa jihar Oyo.
Ana saran babban taron jami’iyyar ta PDP zai gudana daga 15 zuwa 16 ga Nuwambar shekarar da muke ciki.