
Hukumar gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria (MAAUN) dake Kano ta bayar da umarnin gaggawa na rufewar gidajen kwanan dalibai mata da ke Al-Ansar Indabo da ke Hotoro da titin UDB a birnin Kano. Wannan mataki ya biyo bayan zarge-zargen aikata rashin tarbiyya da rashin bin ka’idojin jami’ar.
Hakan na cikin wata sanarwa ce da Dakta Hamza Garba, Mataimakin Shugaban Jami’ar da ke kula da Rayuwar Dalibai, ya fitar a ranar Lahadi.
Mataimakin Shugaban ya ce, matakin rufe gidajen kwanan wani bangare ne na kokarin jami’ar na tabbatar da tsaro, aminci da kuma kula da lafiyar dalibai, tare da tabbatar da cewa ba za a yarda da kowanne irin dabi’ar rashin tarbiyya ba.
“Na samu umarni daga hukumar gudanarwa na rubuta wannan sako don sanar da iyaye da dalibanmu masu daraja cewa jami’a ta janye amincewarta da GIDAJEN KWANAN DALIBAI MATA NA AL-ANSAR INDABO da ke titin UDB da Hotoro.
“Wannan mataki na rufewar gidajen kwana ya biyo bayan rashin bin ka’idoji da dokokin da jami’ar ta shimfida ne game da tafiyar da gidajen kwana na masu zaman kansu.
“Rashin bin ka’idojin ya haifar da abubuwa da ba su dace ba a cikin gidajen kwana, kamar aikata alfasha, rashin wadataccen ruwa da wutar lantarki, rigima tsakanin dalibai, yawo ba tare da izini ba a cikin dare, da kuma amfani da kayan more rayuwa tare da wasu mutane da ba a san su ba, wanda ke barazana ga lafiyar daliban.” In ji Dakta Garba
Sanarwar ta kuma umarci dukkanin daliban da abin ya shafa da su bar gidan kwana nan take bayan kammala jarabawa, kuma su guji ci gaba da zama ko hulɗa da gidajen don kare lafiyarsu da tsaronsu, yayin da hukumar jami’a ke aiki tare da hukumomin tsaro domin tabbatar da cikakken bin wannan umarni.
Jami’ar ta tabbatarwa da iyaye da dalibai cewa za ta ci gaba da kokarin tabbatar da samar da yanayi mai kyau da tsaro domin dalibai.