Gwamnatin jihar Kano ta ce jami’ar Bayero ce ta nemi taimakon ta domin tashin ‘yan kama wuri zauna a unguwar Rimin Zakara.
Kwamishinan yada Labarai na Kano, Ibrahim Abdullahi Wayya ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema Labarai ranar Litinin.
Ya ce a zaman majalisa da aka yi gwamnan Kano ya amince a bai wa jami’ar Bayero filayenta wanda ‘yan kama wuri zauna su ka yi kaka gida.
Wayya, ya kara da cewa sai da aka sanar da mutanen da ke zaune cewa su tashi amma sai batagari suka shiga ciki domin cutar da jami’an tsaro da masu aiki.
Ya ce yinkurin cutar da jami’an tsaro da batagarin su ka yi shi ne ya haddasa mutuwar mutane yayin aikin.
Kwamishinan yada labaran, ya kuma ce kai tsaye ba za a ce ga laifin jami’an tsaro ba domin su ma akwai jami’an da aka jiwa ciwo da yanzu haka suke kwance a asibiti.
Ya kuma ce gwamnatin jihar Kano za ta gudanar da bincike domin gano musabbabin rikicin.
Ya ce filayen mallakin jami’ar Bayero ne wanda ta nemi gwamnatin Kano ta shigo ciki domin taimaka mata wajen karbar filayenta.