Mamallakin jami’ar, Hon. Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila ne ya bayyana hakan, lokacin da yake mika takardar nadin ga mai martaba Sarkin ranar Alhamis a fadar sa.
Sumaila ya ce, nadin Sarkin ya biyo bayan irin sadaukarwar sa da kuma jajircewa wajen bunkasa harkar ilimi da sauran fannonin cigaban al’umma.
Kawo yanzu haka Sarkin na Dutse Alhaji Muhammad Hamim Sunusi, shi ne sabon sabon chancilor na jami’ar.
Kuma ana saran samun ci gaba daga bangarensa musamman kokarinsa wajen bayar da gudunmawa a harkokin Ilimi.
