Wayewar garin Juma’a an tashi da jami’an tsaro sun mamaye gidan Sarkin Kano ta hanyar kofar kudu.
Wakilin Premier Radio ya rawaito cikin hotuna da safiyar Juma’a, jami’an tsaro sun datse hanyar shiga fadar ta kofar kudu.
Daga hotunan, mutane sun yi cincirindo don ganewa idonsu abin da ke faruwa daga babban titin da ya ratsa unguwar sai dai hanyar da za ta shiga zuwa kofar fadar ce jami’an tsaron suka datse ba shiga ba fita.
“Tunda fari masarautar ta tsara cewa Sarkin Kano Muhammadu Sunusi zai jagoranci tawaga zuwa raka sabon hakimin Bichi zuwa fadarsa, tare da gudanar da wasu aika-aikace.
“Sai dai a safiyar yau an wayi gari da ganin jami’an tsaro sun tsare gidan Sarkin”. Inji shi.
Umarnin Kotu
Ana hasashen wannan mataki na ‘yan sandan ba zai rasa nasaba da umarnin da wata kotu ta bayar na haramta wa sarkin da kuma gwamnatin Kano ko wani wakilinsu ba na shiga fadar sarkin Bichi a cikin watan Mayu.
Kofin umarnin da aka like a kofar fadar ta sarkin Bichi ta ce, wannan haramci na nan har sai lokacin da ta yanke hukunci kan karar da aka shigar a gabanta kan soke masarutu da gwamnatin jihar.
Har yanzu babu wanda ya ce uffan daga jami’an tsaro da hukumi jihar dangane da wannan lamari