
An wayi gari da ganin jami’an tsaro a harabar gidan Galadiman Kano da ke unguwar Galadanci a karamar hukumar Gwale.
Rahotanni sun bayyana cewa tun cikin daren jiya Alhamis aka hangi jami’an yansanda sun rufe iyakokin da dukkan hanyoyin zuwa gidan na Galadima.
Wannan zuwa ne bayan da ake sa ran Sarkin Kano Muhammad Sunusi nada sabon Galadiman Kano, Mannir Sunusi da kuma raka shi zuwa gidan kamar yadda kamar yadda al’adar masarautar Kano ta tanada.
Haka shi ma sarkin Kano Aminu Ado Bayero yana nadin Alhaji Sunusi Bayero a matsayin Galadima a fadar sarakin an Nassarawa.