
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta yi ƙarin albashi mafi ƙanƙanta ga ma’aikata daga cefa 30,000 zuwa cefa 42,000, wanda ya yi daidai da Naira 108,780 a Najeriya.
Ƙarin albashi na daga cikin matakan gwamnatin domin inganta rayuwar ma’aikata da ƙarfafar su wajen gudanar da ayyukansu na yau da kullum, kamar yadda gwamnatin ta sanar.
Majalisar Ministocin gwamnatin ce ta ɗauki wannan mataki a taron da ta gudanar a ranar Laraba, inda kuma minsitocin suka tattauna hanyoyin da za a tabbatar da cewa ƙarin albashin zai shafi dukkan ma’aikatan gwamnati ba tare da rarrabewa ba.
Wannan mataki ya zo ne bayan da gwamnatin ta lura da ƙaruwar farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi a ƙasar.
Gwamnatin ta bayyana cewa wannan ƙarin albashi zai taimaka wajen rage wahalhalu da ma’aikata ke fuskanta, musamman wajen biyan bukatun yau da kullum kamar abinci, sufuri, da kuma ilimin yara.