
Gwamnatin Nijar ta sanar da ficewarta daga ƙungiyar OIF, wadda ke haɗa ƙasashen da ke amfani da harshen Faransanci.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da gwamnatin ƙasar ta aikewa ofisoshin jakadancinta a ranar Litinin.
Sanarwa na ɗauke da sa hannun Babban Sakataren Gwamnati kasar, ta bayyana cewa kasar ta yanke shawarar janyewa daga wannan ƙungiya.
Sanarwar ta kuma buƙaci jakadun ƙasar da su shaidawa ƙasashen da suke aiki a cikinsu game da wannan mataki.
Tun bayan juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin Bazoum, gwamnatin soji ta fara janye jikinta daga ƙungiyoyin yammacin duniya.

A baya-bayan nan Nijar tare da ƙasashen Mali da Burkina Faso – waɗanda suma ke ƙarƙashin mulkin soji – sun sanar da ficewarsu daga ƙungiyar tattalin arziƙin yammacin Afirka, ECOWAS.
Ficewar Nijar daga OIF na ƙara nuna yadda sabuwar gwamnatin ke ƙoƙarin kawar da tasirin Faransa a harkokin siyasar ƙasar tare da mayar da hankalinta kan sabbin tsare-tsaren hulɗar ƙasa da ƙasa.
Za a ci gaba da sa ido kan tasirin wannan mataki da kuma matakan gaba da gwamnatin ƙasar za ta ɗauka.