Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa ASUU, reshen Nsukka ta ce Gwamnatin tarayya na lalata makomar ilimi a ƙasar nan saboda rashin cika yarjejeniyar shekarar 2009.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a taron manema labarai da ta gudanar a Jami’ar Jihar Benuwe da ke Makurdi, a cewar Kodinatan yankin, Kwamared Christian Opata, ya ce gwamnati ba ta jajirce wajen magance matsalolin da suka shafi ɓangaren ilimi.
Kwamred Christian ya ce an tattauna tare da kulla yarjejeniyoyi da dama tsakanin kungiyar ta ASUU da kuma gwamnati na tsawon shekaru, amma babu wani ci gaba da aka samu.
Kungiyar ta ASUU, ta kuma zargi wasu daga cikin jami’an gwamnati da yaɗa bayanan ƙarya game da tattaunawar, musamman batun biyan bashin albashi da wasu kuɗaɗen da aka riƙe musu.
