Ƙungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta sake nanata buƙatar kafa ƴansandan jihohi domin magance matsalolin da yankin ke fuskanta.
Hakan na cikin sanarwar bayan taro da ƙungiyar ta fitar bayan kammala taron da ta gudanar a Kaduna a ranar Litinin.
Gwamnonin sun yi kira ga majalisar dokokin Najeriya da na jihohi su ɗauki matakan tabbatar da hakan.
Matsalar Tsaro: Gwamnonin Arewa Za Su Yi Muhimmin Taro A Kaduna
Matakin gwamnonin na zuwa ne kwanaki bayan da Shugaban Tinubu ya bayar da umarnin ɗaukar sabbin ƴansanda domin magance matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta.
Cikin wata sanarwa da Shugaba Tinubu ya fitar a makon da ya gabata ya ce zai duba yiwuwar amincewa da kafa ƴansandan jihohin.
