
Sojojin Isra’ila sun sake bude wuta kan Falasɗinawa a Gaza yayin da suke hanyarsu ta zuwa wata cibiyar rarraba kayan jin-ƙai ƙarƙashin gidauniyar agaji ta Gaza, wacce ke samun goyon bayan Amurka da Isra’ila.
Shaidu sun bayyana cewa, ba kawai sojojin Isra’ila ne suka kai hari ba, har ma wata ƙungiyar mayaƙa ta Falasɗinawa da ke da alaƙa da rundunar sojin Isra’ila (IDF) ta afka wa mutanen da ke kokarin samun tallafi.
Rahotanni sun nuna cewa tun bayan fara ayyukan gidauniyar agaji ta Gaza, cibiyoyin rabon kayan jin-ƙai na fuskantar hare-hare akai-akai.
Ma’aikatar lafiya a Gaza ta tabbatar da mutuwar mutum shida a harin, yayin da har yanzu rundunar sojin Isra’ila ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.
A ‘yan kwanakin da suka gabata, Firaministan Isra’ila ya bayyana cewa ƙasarsa tana mara wa ƙungiyoyin ‘yan bindiga a Gaza baya, a matsayin hamayya ga Hamas.