
Rahotanni daga Gaza sun tabbatar da cewa rundunar sojin Isra’ila ta kai sabbin hare-hare da suka yi sanadin mutuwar iyalai Falasdinawa, ciki har da ma’aurata da ƴaƴansu uku a yankin Mawasi Al’Qarara da kudancin Khan Younis.
A wani harin daban da ya auku a Jabalia, an kashe mutum guda tare da jikkata wasu da dama, kamar yadda jami’an lafiya suka tabbatar.
Hare-haren sun ci gaba da daukar rayuka a safiyar Litinin, inda aka kashe akalla ƴan jarida biyar, ciki har da mai ɗaukar hoto na kafar Al-Jazeera, a wani farmaki da ya auka a asibitin Nasser da ke kudancin Gaza.
Harin ya kuma yi sanadin mutuwar Falasdinawa 15 da ke jinya a asibitin.