
Kwamitin bincike na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce ƙasar Isra’ila ta aikata kisan kiyashi a kan Palasɗinawa a Gaza.
Sabon rahoton ya ce an samu isassun hujjojin da ke nuna cewa, an aikata huɗu a cikin abubuwa biyar na ayyukan kisan kiyashi a ƙarƙashin dokar ƙasa da ƙasa, tun fara yaƙi a kan Hamas a shekarar 2023.
Abubuwa huɗun sun kunshi kashe wasu rukunin mutane, jikkatasu matuƙa tare da janyo musu matsalar da ta shafi lafiyar ƙwaƙwalwa, aikata abubuwa da gangan don ɗaiɗaita su da kuma hana su haihuwa.
Rahoton ya ba da misalai da kalaman shugabannin Isra’ila da yadda suke tafiyar da dakarun tsaron ƙasar, a matsayin hujjar da ke nuni da aniyar aikata kisan kiyashi.
Sai dai ma’aikatar harkokin wajen Isra’ilar ta yi fatali da rahoton, tana mai bayyana shi a matsayin mara tushe balle makama.