Iran ta nemi taimakon ƙasashen waje wajen don kashe wata gobarar daji da ke neman lalata gandun daji mai tsohon tarihi da UNESCO ta ayyana a matsayin abin alkintawa na Tarihi.
Wutar ta tashi ne a dajin tun farkon watan Nuwamba wadda aka fara kashewa, sai kuma ta sake kamawa a ranar 15 ga watan nan, a cewar Kamfanin Dillancin Labarai, IRNA.
Ta kuma ci gaba da ci tsawon kwanaki da dama, a cewar rahoton kafofin watsa labarai na cikin gida.
Sakamakon rashin yiwuwar shawo kan wutar, Iran ta nemi gaggawar taimako daga ƙasashe kawayenta, a cewar Mohammad Jafar Ghaempanah, Mataimaki ga Shugaban Iran Massoud Pezeshkian a shafinsa na X.
Shina Ansari, shugabar Hukumar Kare Muhalli ta Iran, ita ma ta koka. “Ana turo jirage masu zuba ruwa guda biyu na musamman, da wani jirgin sama na helikwafta, tare da mutane takwas daga Turkiyya.
“Idan ya zama dole, za mu nemi taimako daga Rasha ma.” In ji shugabar a hirarta da gidan talabijin gwamnatin kasar.
Gandun dajin na Hyrcanian na shimfiɗa ne tsawon kusan kilomita 1,000 a bakin tekun Iran na tekun Caspian da ya shiga har cikin ƙasar Azerbaijan maƙwabciyarta.
UNESCO ta amince da waɗannan ganduna a matsayin Gadar Tarihi a 2019, tana ganin su na musamman ne saboda tsufarsu da aka kimanta tsakanin shekaru miliyan 25 zuwa 50 da kuma yalwar jinsunan halittu da kuma nau’ikan tsirrai 3,200.
Ana zargin zargin cewa farautawa ne suka kunna wutar a yankin duwatsu na Elit da ke lardin Mazandaran, a arewacin Iran a inda dajin yake.
Ƙasar na fuskantar ɗaya daga cikin munanan ƙauracewar ruwan sama da fari tun bayan fara adana bayanai kusan shekaru sittin da suka gabata.
Daraktan Kula Da Harkokin Gaggawa Na Lardin Mazandaran, Hossein Ali Mohammadi, ya bayyana aikin kashe wutar da cewa ɗaya ne daga cikin mafi rikitarwa a ‘yan shekarun nan.
Kaveh Madani, wani masanin kimiyya na Majalisar Ɗinkin Duniya kuma tsohon jami’in muhalli na Iran, ya bayyana gobarar da cewa ‘Yan Iran na daf da rasa muhimmin abin tarihi wanda ya fi tsohuwar daular Farisa dadewa,” In ji wallafa a X.
UNESCO ta bayyana a shafinta na yanar gizo cewa, gandun dajin Hyrcanian na ɗauke da “adadi mai yawa na tsirrai masu wuya a samu da waɗanda ba su wan
