Iran ta sanar da aiwatar da hukuncin kisa ga mutumin da aka kama yana yi wa Isra’ila leƙen asiri a kasar.
Hukumar Kasar ta ce, an kama Esmail Fekri a shekarar 2023 yana ƙoƙarin miƙa wa Isra’ila bayanan sirrin kasar don samun kuɗi.
Wannan shi ne karo na uku a baya-baya nan da Iran ke aiwatar da hukuncin kisa ga wandan da ta ke tuhuma da zargin leƙen asiri ga Isra’ila.
Babban alƙalin Iran, Gholamhossein Mohseni Ejei, ya bayyana a ranar Litinin cewa, la’akari da yanayin “yaƙi” da suke ciki, dole ne a gudanar da shari’o’i ga waɗanda ake zargin suna aiki da Isra’ila cikin hanzari.
A wani labara kuma, a ranar Lahadi Isra’ila ita ma ta ce ta kama wasu ‘yan ƙasa biyu da a bisa zargin aiki da hukumar leƙen asirin Iran a kasarta
